Ebola: Mataimakin Shugaban Saliyo ya kebe kansa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Cutar Ebola ta halaka mutane da dama a Saliyo

Mataimakin shugaban kasar Saliyo, Samuel Sam-Sumana ya shiga kebe kansa daga sauran jama'a na tsawon kwana 21 bayan cutar Ebola ta yi sanadin mutuwar wani mukarrabinsa.

Kazalika mahukuntan kasar sun kara tsaurara matakai a kasar sakamakon karuwar masu harbuwa da cutar.

Matakan dai sun hada da auna lafiyar jama'a da takaita yawan mutanen da za a dinga dauka a motar haya da kuma wasu matakai a harkar sufurin ruwan kasar.