Matasa sun kone budurwa kurmus a Bauchi

Rahotanni daga jihar Bauchi a Najeriya sun ce wasu matasa sun banka wa wata budurwa wuta suka kone ta kurmus bisa zargin cewa tana dauke da bama-bamai.

An kone ta ne a lokacin da take shirin shiga daya daga cikin manyan kasuwannin birnin, watau Kasuwar Muda-Lawal.

To amma daga bisani jami'an tsaro da shaidu sun bayyana cewa ba a samu bama-bamai tattare da matar ba.

Bayanai sun nuna cewa matasan sun buge ta ne har ta mutu kana suka banka mata wuta ta kone kurmus ta hanyar sa mata taya.

Ganau sun ce matar ta yi shiga irin ta maza kuma tana dauke da kwalabe.

Sun ce an nemi a caje ta kafin ta shiga kasuwar, amma taki yarda -- lamarin da yasa matasan suka yi zargin cewa tana dauke da bama-bamai, suka kashe ta.

Rundunar 'yan sandan jihar ta Bauchi ta bayyana cewa lokacin da jami'an tsaro suka binciki gawarta da ma illahirin yankin basu samu wani abu da ya jibinci bam ba.

Kakakin rundunar DSP Haruna Muhammad ya ce ana kokarin kamo wadanda suka kashe ta.

A baya-bayan nan dai ana samun karuwar hare-haren bama-bamai a tashoshin mota da kasuwanni a arewacin Najeriya -- hare-haren da ake dangantawa da 'yan Boko Haram.

A cikin makon da ya gabata kadai an bada labarin kashe mutane kimanin 90 a garuruwa da birane kamar Kano da Potiskum da Jos da kuma Biu.

Karin bayani