Kudin ajiyar Nigeria na kasashen waje ya ragu

Hakkin mallakar hoto hausa
Image caption Tattalin arzikin Nigeria na fuskantar barazana saboda faduwar darajar kudin kasar

Wasu bayanai da suka fito daga babban bankin Najeriya sun nuna cewa kudaden da ke asusun ajiya na kasashen wajen na kasar sun ragu da kashi takwas cikin dari a cikin watanni biyu kawai.

Kudaden ajiyar wadanda yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 35 da miliyan 13 a ranar 19 ga watan Disamban bara, sun koma dala biliyan 32 da miliyan 30 zuwa ranar sha tara ga watan Fabrairu.

Sai dai minista a ma'aikatar kudin kasar Ambasada Bashir Yuguda ya ce hakan ya faru ne sakamakon faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

Ya kuma kara da cewa 'asusun yana dangana ne da kudin dala, idan dala ta fadi babu shakka (asusun) zai fadi' in ji Bashir Yuguda

Minista Yuguda ya kuma ce babu wasu kudaden Nigeria da suka yi layar zana sabanin abinda wasu ke cewa.