Boko Haram ta kai hari a kusa da Bosso

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wannan shi ne karo na biyu da Boko Haram ta kai hari a yankin na Bosso

Rahotanni daga garin Bosso na Jamhuriyar Nijar na cewa 'yan Boko Haram sun kai hari a yankin.

Wakiliyar BBC a yankin ta ce an kai harin ne a wani kauye mai suna Kurikilewa da ke da nisan kilomita 20 daga Bosso da almurun ranar Lahadi.

Ta kara da cewa 'yan Boko Haram din sun kashe mutane da dama tare da banka wa garin wuta.

A watan jiya ne dai 'yan kungiyar suka kai harin farko a Jamhuriyar ta Nijar, bayan shugabansu ya sha alwashin yin hakan.

Gwamnatin kasar dai ta ce ta kashe 'yan kungiyar da dama, tana mai shan alwashin kawar da su daga kasar.