Gobara ta yi barna a kan tsaunukan Cape Town

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption An kwashe mutanen yankin

'Yan kwana-kwana fiye da 100 a kasar Afrika ta Kudu suna kokarin kashe wutar daji a kan tsaunukan da ke kusa da birnin Cape Town.

Gobarar ta lakume wurare da dama da kuma wasu gidajen.

Hukumomi sun ce ana jinyar mutane fiye da 50 wadanda suka shaki hayaki.

A ranar Lahadi gobarar ta tashi sannan guguwa mai karfi ta kara yada ta.

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Dan kwana-kwana daya ya ji rauni

A rufe hanyoyin mota a yankin saboda rashin kyawun yanayi.

Jirage masu saukar angulu hudu na shawagi a yanki tare fesa ruwa domin kashe wutar.

A kan samu gobara a wannan yankin daga watan Nuwamba zuwa Mayu, lokacin da yanayin wurin keda zafi sosai sannan kuma ga guguwa mai karfi.