Dakarun Nigeria sun kwato garin Gujba

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Dakarun Nigeria na dauki ba dadi da mayakan Boko Harama a Arewa maso gabashin kasar

Rundunar sojin Nigeria ta ce ta kwato garin Gujba na jihar Yobe daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Hakan na zuwa ne bayan da rundunar ta yi shelar kwace garin Gulani daga wajen Boko Haram a makon da ya gabata.

Kawo yanzu babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan ikirarin, amma a cikin 'yan makonnin nan dakarun Nigeria sun sanarda kubutar da garuruwa da dama wadanda a baya suke hannun Boko Haram.

Daga cikin garuruwan da aka kwato akwai Gulak da Madagali da kuma Mubi a jihar Adamawa da kuma Baga da Gambarou a jihar Borno.

An shafe fiye da shekaru biyar ana yaki da Boko Haram a Nigeria, kafin rikicin ya fantsama zuwa makwabtan kasashe kamar Jamhuriyar Nijar da Kamaru da kuma Chadi.