Farashin mai na tasiri a kasuwancin tufa a Nigeria

Faduwar farashin man fetur a kasuwar duniya na tasiri ga mata a jihar Kano wadanda ke sha'awar sayen tufafin kawa.

Birnin Kano da ke arewacin Nigeria na da nisan gaske da rijiyoyin mai da ke kudu amma abubuwan da ke wakana a kudancin na tasiri a arewaci.

"Na zo sayen riga," in ji Halima Sani, wata ma'aikaciya wacce ta shiga shagon sayar da tufa.

"A baya idan kana iya sayen riguna biyu ko uku, amma a yanzu daya kawai zan iya saya."

Farashin tufa a shagon Alhayat Global Synergy ya tashi saboda faduwar darajar kudin Nigeria watau Naira.

Image caption Daga Dubai ake kawo galibin kayayyakin shagon Alhayat Global Synergy

Da farko da ta shiga shagon, ta dauka tana da isashen kudi, amma kuma sai ta ga farashin ya yi sama.

"Sai da na koma gida na kara samun kudi sannan na iya sayen rigar a kan naira 8,000," in ji Halima.

'Korafi'

Mai shagon tufan, Aminu Tanko Kyaure, yana sayo kayayyakin ne daga Dubai.

Akwai leshi da jakunkuna da gwala-gwalai da talakalma wadanda ya ke yo kwantena daga Dubai wanda ke shafe kwanaki 45 kafin isowa Nigeria.

Image caption Aminu Tanko Kyaure ya shawarcin gwamnati ta fadada hanyoyin samunta

"Kafin faduwar darajar naira, Alhamdulillah muna cin kasuwa," in ji Kyaure.

Amma a yanzu farashin dakon kaya daga Dubai zuwa Lagos ya karu sannan kuma kudin mota daga Lagos zuwa Kano shi ma ya tashi.

A cewarsa yana tunanin dage tafiyarsa zuwa Dubai a nan gaba saboda rashin tabbas a kan kudin kasar.

Bintu Usman wacce ke da shago a kan titin Maiduguri Road ta ce lamarin babu dadi.

" A baya ina zuwa Dubai da India amma saboda dalar Amurka ta tashi, a yanzu abubuwa sun tsaya ciki," in ji Bintu.

"Watanni uku kenan ban je ko'ina ba kuma bani da kaya a kasa."

'Sayayya ta Intanet'

Kyaure ya ce zai iya sayayye ta intanet domin rage kudin da zai kashe amma kuma ya fi son ya ce ya ga kayan da idonsa ya taba da hannu kafin ya biya.

"A wasu lokutan kana son ka je ka taba kayan da hannunka domin sanin ingancin tufa kafin ka biyar kudi."

Nigeria na samun fiye da kashi 75 na kudin shigarta daga mai kuma farashin mai ya fadi a watanni shida da suka wuce.

"Shawarata ga gwamnati shi ne ta nemo wasu hanyoyin samun kudaden shiga," in ji Kyaure domin kaucewa fadawa irin wannan matsalar.

A bangaren tufa, faduwar darajar naira na mummunan tasiri ga wannan kasuwancin.

Kuma a yanzu haka masu shagunan tufa a Kano suna ji a jikinsu.