Shugaban Namibia ya lashe kyautar Mo Ibrahim

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hifikepunye Pohamba zai karbi kyautar $5m saboda gudanar da mulki na gari a Namibia

Shugaban kasar Namibia mai-barin-gado, Hifikepunye Pohamba, ya lashe kyautar Mo Ibrahim a kan mulki na gari.

Duk shugaban kasar da ya lashe kyautar dai zai karbi kyautar $5m (£3.2m).

Sai dai an kwashe shekaru hudu a jere ba a samu shugaban da ya lashe kyautar ba saboda, a cewar masu bayar da ita, ba a samu shugaban wata kasa a Africa ba da ya gudanar da mulki na gari a cikin shekarun.

Mr Pohamba, tsohon dan tawaye ne wanda ya yi fafutikar ganin kasarsa ta samu 'yancin-kai, kuma ya yi wa'adi biyu na shugabancin kasar.

An soma zabarsa a shekarar 2004, sannan aka sake zabensa a shekarar 2009.

Hage Geingob shi ne mutumin da aka zaba domin ya maye gurbinsa bayan zaben da ya lashe.