An soma karancin man fetur a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan bumburutu na cin kasuwarsu

An soma fuskantar wahalar samun man fetur a jihohi da dama a Najeriya tun daga karshen makon jiya, lamarin da ya tilasta wa mutane shafe lokaci mai tsawo suna bin dogayen layuka.

A wasu wuraren ana sayar da man a kan farashin da ya wuce na hukuma, watau a maimakon N87 kowacce lita ana sayarwa ne a kan kusan N100 kowacce litar mai.

Bayanai sun ce ana fama da karancin man fetur din ne a jihohin Lagos da Kano da Imo da Kaduna da Niger da Nasarawa da Kwara da Katsina da kuma Abuja babban birnin kasar.

Lamarin ya kara muni ne saboda gidajen mai kadan ne suka sayar da man a yayin da wasu kuma suke a rufe.

Kawo yanzu hukumomi a Nigeria ba su bayyana dalilan da suka janyo karancin man ba.

Najeriya dai ita ce kasa ta shida mafiya arzikin man fetur, sai dai duk da haka 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.