Ukraine na cikin mummunan hali — UN

Hakkin mallakar hoto
Image caption Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane 6000 ne suka mutu a Ukraine

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa gabashin Ukraine na cikin mummunan hali, tana mai cewa akalla mutane 6000 aka kashe a yankin.

A wani rahoto da Ofishinta da ke kula da hakkin Dan-Adam ya fitar, Majalisar ta ce mutane na cikin matsanancin hali, sannan an rusa duk abubuwan more rayuwa sanadiyar rikicin da ake yi.

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya da ke sa ido a kan rikicin kasar sun ce ana ci gaba da aikewa da makamai zuwa yankin gabashin Ukraine daga kasar Rasha duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka sanya wa hannu a watan Fabrairu.

An fitar da wannan rahoto ne a daidai lokacin da Sakataren wajen Amurka, John Kerry ke gana wa da takwaransa na Rasha, Sergei Lavrov a kan rikicin Ukraine da kuma kisan da aka yi wa wani dan adawar Rasha, Boris Nemtsov.