Boko Haram: Dakarun hadin gwiwa za su fara aiki

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dakarun kawancen za su kasance karkashin jagorancin janar dan Najeriya

A karshen watan Maris din da muke ciki ne ake sa ran dakarun hadin gwiwa da za su fara yaki da kungiyar Boko Haram za su fara aiki.

Hakan ya biyo bayan kammala shirin kafa dakarun kawancen na kasashen Nigeria da makwabtanta, Nijar da Chadi da Kamaru da kuma Benin.

Sai dai menene yiwuwar cewa ko sojojin 8,700 za su iya kawo karshen Boko Haram, kungiyar da ta yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane?

Karan tsaye na farko shi ne wuraren da dakarun za su iya shiga.

Wasu majiyoyi na soji da kuma na diplomasiyya sun tabbatar da cewa dakarun da aka yi wa lakabi da MNJTF za su yi aiki ne a wajen garin Diffa da ke bakin iyakar Nijar da kuma garuruwan Baga da Gamboru a Najeriya.

Abin nufi a nan shi ne dakarun kawancen za su tabbatar da tsaro ne kawai a bakin tafkin Chadi wanda kashi "10 zuwa 15 cikin dari ne na wuraren da Boko Haram suke ayyukansu. " In ji majiyar diplomasiyya da ke yankin wanda bai so a bayyana sunansa ba.

"Wannan shirin ba zai magance matsalar ba, ya rage wa Najeriya ta karasa sauran aikin." A cewar majiyar.

A hakikanin gaskiya Najeriya ba ta so sojojin kasashen waje su shiga kasarta.

Abin da ya sa ba a tabbatar da ko sojojin Nijar da na Kamaru za su shiga cikin Najeriya su yi yaki kamar yadda sojojin Chadi ke yi.

Najeriya za ta samar da dakaru 3,250, Chadi dakaru, 3000 yayin da Kamaru za ta samar da dakaru 950 sai Nijar 750, ita ma Benin dakaru 750.

Da zarar dai kungiyar ta AU ta amince da shirin, za a rarrabawa dakarun wuraren da za su yi aiki.