Mata fiye da 2,000 sun fice daga Ghana

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumomin Ghana sun ce ba su taba ganin mata da yawa haka sun bar kasar ba

Hukumar shige-da-fice ta Ghana ta ce a 'yan watannin nan, yawan mata matasa na kasar da ke ficewa zuwa wadansu kasashen fiye ya haura na ko wanne lokaci a baya.

Hukumar ta ce daga watan Satumban bara zuwa yanzu, mata fiye da dubu biyu ne suka bar kasar da nufin zuwa neman aiki a kasashen waje.

Kasashen da matan ke kwarara sun hada da Kuwait, da Saudi Arabia, da Qatar, da sauran kasashen Gabas ta Tsakiya.

A cewar kakakin hukumar, Francis Pamdeti, su kan ga mata 15 ko 20 masu zuwa kasa daya a cikin kasashen na Gabas ta Tsakiya.

"Idan muka tqambaye su abin da za su je yi, sai su ce an yi musu alkawarin samo musu aikin yi a kasashen", inji shi.

Sai dai kuma ya ce labarin da suke samu daga wasu matan da ke dawowa gida ba mai dadin ji ba ne--matan na bayar da labarin yadda aka ci zarafinsu ta hanyar lalata da barin su da yunwa.