'Yan Boko Haram na shirin fada da sojoji a Gwoza'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Nigeria na ci gaba da yakar Kungiyar Boko Haram

Rahotanni daga Gwoza a jihar Borno na cewa 'yan Boko da ke iko da garin sun umarci mata da yara su fice daga garin a yayin da suke shirin fafatawa da sojojin Nigeria.

Wata mata da ta tsere daga garin ta shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram sun hallaka mutane da dama a Gwoza.

'yan Boko Haram din sun hallaka tsofaffi maza ne ta hanayr harbe su da bindiga, a cewar matar.

Sanata mai wakiltar garin Gwoza ya tabbatar wa da BBC irin ta'asar da 'yan Kungiyar Boko Haram din suke aikatawa a garin.

Sanata Muhammad Ali Ndume ya ce 'yan kungiyar Boko Haram na shirin fafatawa da sojoji, kuma sun gwammace su mutu a madadin su tsere daga garin.