Yadda masu jihadi ke jan ra'ayin 'yan mata a Turai

Ayesha ta ce an tuntube ta ne ta shafin Facebook
Bayanan hoto,

Ayesha ta ce an tuntube ta ne ta shafin Facebook

Mayaka masu da'awar jihadi da ke da "kyau" na jan hankalin mata Musulmai 'yan Biritaniya, in ji wata mai tsattsauran ra'ayi da ta sauya ra'ayi.

Ayesha wadda aka sakaya sunanta na gaskiya, ta shaida wa shirin BBC Newsnight, cewa an nuna musu cewa su dunga kallon Biritaniya a matsayin "makiyarsu".

Yanzu ta dawo daga rakiyar irin wannan ra'ayin, amma ta ce sauran kawayenta da suka shiga kungiyar na kallon "Jihadi John" a matsayin "gwarzo".

A kwanan nan wasu 'yan mata suka bar London suka wuce Syria domin hadewa da kungiyar mayakan IS.

Ayesha daga yankin Midlands, wadda a yanzu take da shekaru 20, ta ce wani mai ikirarin jihadi ya tuntube ta ne lokacin ta na da shekaru 16 zuwa 17.

Ta ce mutumin ya tura mata sako ta Facebook inda ya ce mata tana da "matukar kyau" kuma lokaci ya yi da za ta "lullube kyawunta."

A cewar Ayesha suna amfani da addinni inda ake cewa mace idan ba ta yarda ba, za ta "shiga wuta".

'Zumudi'

A cewarta akwai ban sha'awa da kuma tsoro a abin da ta gani.

"A matsayina na matashiya, ina son in hadu da masoyi na, kuma a duka hotunan bidiyon da suka wallafa a YouTube, galibin mayakan na da kyau suna da ban sha'awa".

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Mayakan al-Shabab na daga cikin wadanda suka ja ra'ayin Ayesha

"Akwai jin dadi da zumudi saboda mutum zai samu wanda suke addinni daya ko da ba kabilarsu ba daya ba".

Ta kara da cewar : "Abin tamkar a ce ka samu masoyinka ne kafin ya rasu, kuma zai mutu a matsayin shahidi, kuma zamu hadu a Aljannah".

An sauya wa Ayesha ra'ayinta ne kafin bullar kungiyar IS wadda ke da iko da wasu yankunan Iraki da Syria, inda a lokacin take sha'awar mayakan al-Qaeda da na al-Shabab.

'Ka da a amince da Biritaniya'

"A wasu hudubar da ake yi, ana karfafa mana gwiwa cewa ka da mu ce mu 'yan Biritaniya ne," in ji Ayesha.

Ta kara da cewar an gaya mata ta dunga kallon Biritaniya a matsayin "kasar kafirai" wadda ta kashe Musulmai da dama kuma "a bar ki ce".

"Kada ku amince da gwamnati da 'yan sanda kuma kada ku kai 'ya'yanku makarantun gwamnati," ta kara da cewa.

Amma daga bisani Ayesha ta yi tur da wannan ra'ayin.

Ta ce abubuwa biyu ne suka sa ta fitar da ita daga wannan ra'ayin, na farko ba a yi wa mata "adalci" sannan mabiya kungiyar "na zuwa su kashe wadanda ba Musulmi ba".

Ayesha ta ce tsaffin kawayanta za su jinjina wa Mohammed Emwazi wanda ake kira "Jihadi John" wanda ake nuna wa a bidiyo ya na fille kawunan mutane.

A cewarta "mutum ne da suke alfahari da shi."