Netanyahu ya ce Iran barazana ce ga 'duniya'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan majalisar sun jinjina wa Mr Netanyahu

Firayi Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi kakkausar suka kan yarjejeniyar da ake shirin kulla wa tsakanin kasashen yammacin duniya da kasar Iran kan batun nukiliyar Iran din.

A jawabinsa ga majalisar dokokin Amurka, Netanyahu ya ce dole ne duniya ta kasance wuri guda domin hana abin da ya kira yunkurin Iran na kama hanyar ta'addanci.

A cewarsa Iran dama can abokiyar gaban Amurka ce, kuma yaki da kungiyar IS ba zai sa su zama abokai ba.

Domin cin galaba kan kungiyar IS sannan a bai wa Iran damar mallakar nukiliya, a cewarsa hakan zai zama tamkar samun nasara ne a gwagwarmaya amma kuma rashin nasara a yaki.

'Yan majalisar sun jinjinawa Mr Netanyahu inda suka mike tsaye, a yayinda wasu 'yan jam'iyyar Democrat suka kauracewa zaman.