'Mafi yawan mutane ba sa samun maganin rage radadi'

Hakkin mallakar hoto Other

Hukumar sa ido kan miyagun kwayoyi ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi uku bisa hudu na mutanen duniya ba sa iya samun magungunan rage radadi kamar Morphine.

A wani rahoton da ta ke fitarwa duk shekara, hukumar ta ce kashi 17 cikin dari ne kacal na mutanen duniya ke shanye fiye da kashi 90 na maganin rage radadi na morphine da ake samarwa.

Kuma akasari masu yin amfani da magungunan mazauna arewacin Amurka da yammacin Turai da Australia da New Zealand ne.

Rahoton ya kuma fito da yadda ake ci gaba da amfani da wani sinadari wanda da shi ake samar da hodar koken ba bisa ka'ida ba, musamman a yammacin Turai da kuma irin mace-macen da hakan ke haifarwa.

Rahoton ya sake yin gargadi game da yiwuwar karuwar amfani da wasu miyagun kwayoyi a nahiyar Turai.