Amurka da Isra'ila sun samu sabani —Obama

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Obama ya ce ziyarar Benjamin Netanyahu ta zo a lokacin da bai dace ba

Shugaba Obama ya ce akwai sabanin ra'ayi babba a tsakanin Amurka da Isra'ila dangane da hanyar da ya kamata a bi don hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Amma a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Reuters gabanin wani jawabi da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai yi wa majalisar dokokin kasar, Mista Obama ya ce ba ya zaton sabanin zai yi wa danganatakar da ke tsakanin kawayen biyu illa ta dindindin.

"Ba na zaton wannan sabani ya yi wata illa ta har abada. Ina dai ganin ya dauke hankali daga abin da ya kamata a ce mun mayar da hankali a kansa, wato yadda za mu yi mu hana Iran mallakar makamin nukiliya".

Mista Obama dai na so ne a dakatar da shirin nukiliya na Iran har tsawon shekaru goma, yayin da Isra'ila ke ganin cewa akwai hadari a duk wata yarjejeniya da za ta kyale Iran da tashoshin nukiliyar da za su iya aiki.