Ana kazamin fada a birnin Aleppo na Syria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekaru uku kenan ana fafatawa tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye a Syria

Rahotannin daga Syria na cewa an kashe 'yan tawayen kasar da dakarun tsaro da dama a wani kazamin fada da ake yi a birnin Aleppo.

A cewar kungiyar kare hakkin dan adam ta Syria mai cibiya a Biritaniya, an fara fadan ne lokacin da wani babban bam da aka dasa a shalkwatar leken asiri ta sojin sama ya fashe.

'Yan tawayen sun tona rami ne ta karkashin kasa inda suka bi, suka dasa bam din.

Sun kuma bi bayan tashin bam din da kai hare-hare ta kasa.

'Yan tawayen dai na ci gaba da fada da dakarun tsaro don kwace ikon Aleppo tun da aka fara yakin basasar kasar Syria.