Anya Boko Haram ba ta da alaka da IS?

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Kungiyar Boko Haram ta fadada ayyukanta zuwa kasashen da ke makoftaka da Nigeria.

Alamu na ci gaba da bayyana da ke nuna yiwuwar kungiyar IS tana tasiri a kan yadda kungiyar Boko Haram ke shirya faya-fayen bidiyon ta da aikace aikacenta da kuma yin amfani da shafin sada zumunta na Twitter.

A can baya dai kungiyar Boko Haram ba ta da shafin yada ayyukanta ta intanet, amma daga ranar 18 ga watan Janairun shekarar nan, aka samu wani shafin Twitter mai suna "Al-Urwah Al-Wuthqa'' da aka yi amanna na Boko Haram ne, kuma wasu kusoshin kungiyar IS suka rika tallata shi.

Kazalika yadda kungiyar ke wallafa hotunan bidiyo da su ke kamanceceniya da wanda kungiyar masu fafutukar kafa daular musulunci a kasashen Iraqi da Syria wato IS ke wallafawa a shafukan Internet abin tambaya ne.

Hoton bidiyo na baya-bayan nan da kungiyar Boko Haram ta sanya wanda ya nuna yadda suka fille kan wasu mutane biyu da suka yi garkuwa da su, a iya cewa irinsa ne mayakan IS suka wallafa na fille kawunan wasu mutane biyu da suke zargin 'yan leken asiri ne.