Ghana za ta binciki sanadin gobarar jirgin Mahama

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane a Ghana za su so su ji abin da ya haddasa gobarar

Gwamnatin Ghana ta ce zata kafa wani kwamiti wanda zai binciki yadda aka yi jirgin saman shugaban kasar, John Dramani Mahama ya kama da wuta a ranar Talata.

Lamarin ya auku ne a filin saukar jiragen sama da ke birnin Accra a dai dai lokacin da jirgin yake shirin tashi zuwa kasar Equatorial Guinea don gudanar da wani aiki na musamman.

Wata sanarwa da rundunan sojan kasar ta fitar bata bayyana ko shugaban kasar yana cikin jirgin lokacin da wutar ta kama ba.

Haka kuma babu karin bayani game da ko su waye a cikin jirgin saman a lokacin da hadarin ya auku.

Ana yawan samun haduran a jiragen sama a nahiyar Afrika abin da wasu ke dangatawa rashin cikakkun matakan kariya.