Sarkin Gusau Kabir Danbaba ya rasu

Hakkin mallakar hoto Gusau Emirates Facebook
Image caption Sarkin ya yi jinya kafin rasuwar tasa

Allah ya yi wa Sarkin Katsinan Gusau da ke jihar Zamfara Alhaji Muhammadu Kabir Danbaba rasuwa a ranar Alhamis.

Mai martaba ya rasu ne bayan kwashe shekaru 31 bisa karagar mulki.

Ya rasu a wani asibiti da ke birnin Abuja yana da shekaru kimanin 91 a duniya.

Kwamishinan watsa labarai na jihar Zamfara Ibrahim Muhammad ya shaida wa BBC cewa za a yi jana'izarsa da misalin karfe tara na dare a babban masalacin Gusau.