Boko Haram: Shugaban Chadi ya ba Shekau zabi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Idriss Deby ya ce ya san wurin da Shekau ke ci gaba da buya

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya bukaci shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya mika wuya ga soji ko kuma a kashe shi.

Mr Deby ya yi ikirarin cewa ya san wurin da Shekau ke boye.

Deby ya bayyana haka ne a lokacin da shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou, ya kai masa ziyara a birnin Ndjamena.

Ya ce, "Idan Abubakar Shekau na son kansa da lafiya, to ya mika wuya; mun san inda yake. Idan bai mika wuya ba, makomarsa za ta zama iri daya da sauran mabiyansa."

Rikicin Boko Haram wanda aka soma a Najeriya a yanzu ya shiga makwabtan kasashe kamarsu Chadi da Kamaru da kuma Nijar.

Mutane fiye da 13,000 ne suka rasu tun da aka soma rikicin Boko Haram a Najeriya.