'Boko Haram na kwaikwayon kungiyar IS'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Zeid Ra'ad Al Hussein na majalisar dinkin duniya

Kwamishina mai lura da kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein ya ce, mayakan kungiyar Boko Haram na amfani da kananan yara mata wajen harin kunar bakin wake.

Mr Zeid ya kuma nuna damuwarsa cewa mayakan na Boko Haram na bin irin salon mayakan IS, na sacewa, da fyade, da kuma bautar da mata da da 'yan mata a irin mummunar ta'asar da suke tafkawa.

Fada tsakanin kungiyar masu tsattsauran ra'ayin da dakarun hadakar kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi ya kara rincabewa a cikin watannin baya bayan nan, wanda ya shafi fararen hula miliyan uku.

A ranar Laraba ne, Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby ya bukaci shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau, ya mika wuya ga soji ko kuma a kashe shi.

Mr Deby ya yi ikirarin cewa ya san wurin da Shekau ke boye.

Mutane fiye da 13,000 ne suka rasu tun da aka soma rikicin Boko Haram a Najeriya.