An sallami mai cutar Ebola ta karshe a Liberia

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption WHO na fatan kwao karshen cutar Ebola a kasashen da ta fi kamari

Kasar Liberia ta sallami wata mata wadda ita ce ta karshe da ke dauke da cutar Ebola, bayan an shafe mako guda bata nuna wata alama ta cutar ba, a cewar hukumar lafiya ta duniya.

Beatrice Yardolo mai shekaru 58 ta bar cibiyar kula da masu cutar Ebola ta 'yan kasar China da ke Monrovia, bayan makonni biyu tana samun kulawa.

Jami'ai sun ce wannan shi ne karon farko da ba a samu wani wanda ya kamu da cutar ba, tun a watan Mayun shekarar 2014.

Kimanin mutane 10,000 ne dai suka mutu sakamakon cutar mafi yawansu a kasashen Guinea da Liberia da kuma Saliyo.