Ambaliyar ruwa za ta karu zuwa 2030

Wani Kauye da ambaliyar ruwa ta wanke Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani Kauye da ambaliyar ruwa ta wanke

Adadin mutanen da ambaliyar ruwa ta koguna kan shafa a duniya zai ninka har sau ukku a cikin shekaru 15 masu zuwa kamar yadda masu nazari suka nuna.

A cewar Cibiyar World Resources Institute, sauyin yanayi da karuwar yawan jama'a sune za su haddasa wannan matsalar.

A Brittaniya, kimanin mutane 76,000 ne a shekara za su fuskanci wannan matsalar ta ambaliyar ruwan muddin dai ba a inganta shingen kariyar Koguna ba.

Tsadar kudin da za a kashe kowacce shekara don wannan aiki a yankunan maraya za ta iya zarce fam billiyan daya.

Cibiyar tace, wannan shine karon farko da masu nazari suka bayyana bayanai da ya shafi duniya a kan ambaliyar ruwa da ake fama da ita a yanzu da kuma nan gaba.

Ta yi nunin cewar wasu mutane miliyan 20 suna cikin hadarin fuskantar ambaliyar ruwan kuma wannan zai ci kudi kimanin fam billiyan 65.

Kamar yadda wani sabon bincike ya nuna, a cikin shekaru 15 wannan adadi na mutanen zai iya kaiwa kimanin miliyan 50 kuma hasarar za ta shafi tattalin arzikin duniya kimanin fam billiyan 340.

Yawancin wannan an danganta shi da sauyin yanayi da cigaban rayuwa da tallain arziki.

Zuwa shekara ta 2030, idan har babu karin kudi na kare afkuwar ambaliyar ruwa, a kowacce shekara gwamnatin Brittaniya za ta rinka kashe sama da fam billiyan 2.

Bankin duniya ya ce wannan kididdiga za ta taimaka wajen ilimantar da gwamnati dangane da dabarun kariya da kawar da ambaliyar ruwan.

Kamar yadda kungiyar agaji ta Red Cross ta nuna kusan rabin bala'il da aka fuskanta a bara ambaliyar ruwa ce ta haddasa shi.

Karin bayani