INEC ta gudanar da zaben gwaji a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kano na cikin jihohin da aka gudanar da zaben na gwaji

A ranar Asabar ne hukumar zabe ta kasa a Nigeria ta gudanar da zabukan gwaji, ta hanyar amfani da na'urar tantance sahihancin zabe da ake cece-kuce a kanta.

Manufar hukumar dai a cewar ta, ita ce tabbatar da ingancin na'urar da amfani da ita, domin gamsar da 'yan Nijeriya cewa za ta yi aiki a lokacin manyan zabukan da za a yi a wannan wata da watan gobe.

A jihohi goma sha biyu aka gudanar da wannan aiki a duk fadin Nigeria, wadanda suka hada da Delta da Rivers da Ekiti da Lagos da Anambra da Ebonyi.

Sauran su ne Nassarawa da Niger da Kano da Kebbi da Bauchi da Taraba.