Shekara guda da batan jirgin Malaysia

'Yan uwan wadanda ke cikin jirgin Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekara guda kenan babu amo babu labarin jirgin MH370.

Shekara guda cif ke nan da masu binciken jirgin samfurin Boeng 777 da kasar Australia ke jagoranta ke ci gaba da gudanar da ayyukan binciken, wala'allah ayi nasarar samun wani abu da za a iya dangantawa da tarkacen jirgin MH370.

Sai dai nan gaba a yau ne ake sa ran wasu kwararru da su ma suka gudanar da binciken kwakwaf a kudancin tekun india, inda aka yi amanna da cewar anan jirgin ya fadi, za su gabatarwa gwamnatin kasar sakamakon binciken da suka yi.

To amma ba wani haske da aka samu da ke nuna ko masu binciken sun gano wata alama ta jirgin, haka nan babu tabbas ko za a samu sabbin bayanai kan dalilin da ya sa jirgin ya bata, jim kadan bayan ya tashi daga filin tashi da saukar jiragen sama na Kuala Lampur.

Prime ministan kasar Najib Razak yace babu wata kalma da za a yi amfani da ita, wadda za ta bayyana halin kunci, da damuwa da iyalan wandan da abin ya rutsa da su ke ciki tsahon wanann lokaci.

Yace babban abin damuwar shi ne rashin samun wata alama, ko dai ta tarkacen jirgin, ko kayan pasinjojin da ke ciki da za a alakanta jirgin MH370, na daga cikin abinda ya kara sanyawa zukata suke cikin kunci.

Masu bincike dai sun gagara gano akwatain adana bayanan jirgin wato Black Box, wanda a cikinsa ne za a ji dukkan bayanai abubuwan da suka faru gabannin fadauwar jirgin.

Haka kuma akalla an bincike sama da kashi 40 cikin 100 na tekun India, wurin da a baya kwararru suka ce sun fara samun alamar akwatin adana bayanan jirgin, daga bisani kuma suka gano ba bu alamar hakan.

A ranar 8 ga watan Maris din shekarar da ta gabata ne jirgin Malaysian samfurin Boeing 777 mai lamba MH 370 dauke da pasinjoji fiye da 239 ya yi batan da har yanzu ba abu amo babu labarinsa.