Dakarun Nijer sun kai wa Boko Haram hari

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Niger ma na fafatawa da Boko Haram

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijer sun ce dakarun kasar da na Chadi na can na kaddamar da hare-hare kan 'yan kungiyar Boko Haram a yankunan da ke iyakar Nijer da Najeriya.

Kasashen ukku dai -- da ma makwabciyarsu Kamaru -- duk suna fama da hare-haren 'yan Boko Haram.

Amma sun ce sun hada kansu domin yakar kungiyar. Da alama farmakin, wanda aka fara kaiwa ranar Asabar da safe, na daga cikin abin da suka tsara.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun Nijer da na Chadin na kai farmakin ta sama da ta kasa.

Mutane da dama a Diffa sun ce sun ga motocin soji cike da dakarun suna dannawa zuwa Najeriya.

Sun ce sun kuma ji karar harbe-harben manyan bindigogi daga bisani.

Wadanda suka ga sa'adda dakarun ke tafiya sun ce sun gansu ne da misalin karfe shidda na safe a ranar Asabar.

Dakarun sun tashi ne daga Rundana ta Biyar da ke yankin Diffa, injisu.

Sun kuma ce al'ummar garin Diffa sun fito da dimbin yawa suna nuna goyon bayansu ga dakarun a lokacin da suke filin dagar.

Karin bayani