Saudiyya tafi kowacce kasa siyan makamai-Rahoto

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sarki Salman na Saudiyya

Wani sabon rahoto kan kudaden da kasashen duniya ke kashewa wajen sayen makamai ya ce kasar Saudiyya ita ce ke sahun gaba a duniya wajen sayen makamai, inda ta zarta kasar Indiya.

Masana harkokin tsaro dai sun ce yawan kudaden da Saudiyya ke kashewa yanzu ta fuskar tsaro ya kai kashi hamsin da hudu cikin dari a shekarar da ta gabata.

A cewar sabon rahoton, kasar Saudiyya ta kashe tsabar kudi har dala biliyan shida da rabi wajen sayen makamai a 2014.

Ana kuma hasashen cewa kudaden ka iya karuwa zuwa dala biliyan 10 a shekarar 2015.

Rahotanni dai na nuna cewa kasar ta Saudiyya tana yin dari-dari da kasar Iran wadda a yanzu haka take kokarin cimma yarjejeniya kan shirinta na makamin nukiliya da manyan kawayen Saudiyyar.