APC za ta kai matar Jonathan kotun ICC

Image caption Amaechi ya ce jam'iyyar APC ba ta son tayar da hankali

Jam'iyar APC a Najeriya ta ce za ta gurfanar da matar shugaban kasar Goodluck Jonathan a gaban kotun aikata laifukan yaki ta duniya, ICC.

A wata sanarwa da shugaban kwamitin kamfe na dan takarar shugabancin kasarta ya fitar, Mr Rotimi Amaechi, ya ce za su dauki matakin ne saboda Mrs Patience Jonathan ta bukaci a rika jifan 'ya'yan jam'iyyar ta APC.

A yanzu haka akwai wani hoton bidiyo da ke yawo a yanar gizo inda matar Mr Jonathan a lokacin wani taron kamfe a birnin Calabar na jihar Cross River take kira ga magoya bayanta cewa, "duk wanda ya zo ya ce muku Canji, to ku jefe shi".

Mr Rotimi Amaechi ya ce wannan kalami ne da ke son tunzura jama'a domin su far ma 'yan jam'iyyar ta APC.

Ya kara da cewa kalaman sun yi kama da na matar tsohon shugaban Cote D'Ivoire, Mrs Simone Gbagbo, wacce ita ma ta rika yin kiraye-kiraye a tashi hankali gabanin zaben kasar na shekarar 2010.

A cewarsa, sun aika ga wasiku ga Babban Sifeton 'yan sandan kasar da hukumar kare hakkin Dan Adam domin su dauki mataki, baya ga shirye shiryen da suke yi na gurfanar da ita a Kotun masu aikata manyan laifuka ta duniya.

Mr Amaechi ya kara da cewa jam'iyyarsu ta APC jam'iyya ce da ke kaunar zaman lafiya domin haka ba za su goyi bayan duk wani mai son tayar da fitina ba.