Matakin Biritaniya kan Musulmai ba ya tasiri

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Niritaniya na damuwa kan yadda matasa ke tafiya don bin sahun IS

Wani tsohon jami'in 'yan sanda a Biritaniya ya ce babban matakin da gwamnati ta dauka na hana sanyawa kananan yara Musulmai tsattsauran ra'ayi ba shi da tasiri.

Dal Babu, wanda musulmi ne, ya ce mafi yawan al'ummomi na ganin hakan a matsayin wata hanya ta leken asirinsu.

Mr Babu ya kara da cewa "Ba bu wadataccen ilimi kan bambamcin addini da kabila, wanda hakan ya kara munana bayan da kananan jami'an 'yan sanda suka aiwatar da wannan matakin."

An kara samun yawaitar bincike kan kokarin hana sanyawa yara tsattsauran ra'ayi, saboda yadda damuwa ke kara yawaita kan yadda daruruwan 'yan Biritaniya ke tafiya zuwa Syria don bin sahun masu da'awar jihadi na kungiyar IS.