2015: Mbeki ya gana da manyan 'yan takara

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Za a fafata tsakanin Shugaba Jonathan mai ci da kuma abokin hamayyarsa Janar Muhammadu Buhari

A Najeriya, tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Thabo Mbeki ya kammala ganawar da ya ke yi da manyan 'yan takarar shugabancin kasar gabanin zaben da ke tafe.

Shi dai Mr Thabo Mbeki ya fara ganawa ne da shugaba Goodluck Jonathan a ranar lahadin data gabata, inda kuma daga bisani ya gana da Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugaban kasa na babbar jam'iyyar adawa ta APC.

A ganawar da ya yi da manyan 'yan takarar biyu, babu wani daga cikinsu da ya amince ya yi wa manema labarai jawabi dangane da irin abubuwan da suka tattauna akai.

Sai dai wata majiya daga bangaren janar Muhammadu Buhari ta shaidawa BBC cewa, Mr. Mbeki ya kai ziyarar ne a madadin Majalisar dinkin duniya inda suka bukaci hukumomin Nigeria su tabbatar da cewa an gudanar da zabe a ranar 28 ga watan Maris kamar yadda aka tsara.

Majiyar ta kara da cewa majalisar dinkin duniya ta nemi a dauki dukkanin matakan da suka wajaba domin kaucewa tashe tashen hankula a Nigeria a lokacin zabubbukan.