Babu rashin jituwa tsakanin Jonathan da Mu'azu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Jonathan da sauran jiga-jigan PDP a wurin kamfe

Jam'iyyar PDP mai mulkin Nigeria ta musanta rahotannin rashin jituwa tsakanin dan takararta na shugaban kasa, Dr Goodluck Jonathan, da kuma shugaban jam'iyyar na kasa, Dr. Adamu Mu'azu.

Jam'iyyar ta mai da martani ne game da rahotannin da wasu kafafen yada labarai suka wallafa a Nigeria a kan zargin tsamin dangantaka tsakanin Mr Jonathan da kuma Mu'azu.

Sanarwar da kakakin jam'iyyar PDP, Olisa Metuh ya fitar, ta ce Mu'azu a matsayinsa na uban jam'iyya yana aiki tukuru domin ganin ta samu nasara.

Sanarwar ta kara da cewa "Mun san mutanen da ke kokarin kawo rashin jituwa tsakanin shugabanninmu domin kawo mana cikas a kamfe din da muka sa a gaba."

Tun daga shekarar 1999, jam'iyyar PDP ce ke mulkin Nigeria amma a zaben da za a yi a karshen wannan watan, jam'iyyar na fuskantar kalubale mafi girma tun kafuwarta.