Matsalar karancin wajen binne gawa a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan tsohuwar makabartar ta cika babu wuri a Biritaniya

Mutuwa riga ce kuma tabbas kowanne mai rai zai dandani mutuwa. Amma ko mai zai faru bayan an mutu, sai dai akwai babbar matsala da ke fuskanta duniya, watau na karancin wuraren da za a binne mutane bayan sun mutu.

Wakilin BBC na al’amuran yau da kullum John McManus, ya duba kan yadda ake samun matsin lamba sakamakon karancin wuraren binne mutane, da kuma yadda za a magance matsalolin wajen da zai zamo gidanmu na karshe.

Wani babban sauyi da aka samu lokacin da aka daina amfani da bayi aka koma amfani injina a ma’aikatu a karni na 18 da karni na 19, shi ne ya yi sanadiyar da kaurar ‘yan Biritaniya daga kauyuka zuwa birane. A yayin da birani suke cika da mutane, a lokacin ne kuma aka fara samun matsalar karancin in da za a binne matattu.

A da can babu wannan matsalar. Yawanci mutane da suke zama a kauyuka, ana binnesu ne a makarbartu da ke kusa da coci-coci.

A yayin da ake kara samun yawaitar mutane masu zama a birane, hukumomi a zamanin sarauniya Victoria sun yi kokarin samo mafita wajen gina manyan makabartu, yawanci a wajen gari, inda za a binne matattu cikin kwanciyar rai.

Mafitar tayi aiki na dan lokaci. A yanzu kuwa, wadancan makabartun sun cika, sannan kuma karuwar da al’umma ke yi ya na dawo da hannun agogo baya wajen karanci inda za a binne mutane.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Makabartar San Michele da ke tsibirin Venice

Tim Morris, shi ne shugaban hukumar kula da makabartu a Biritaniya, ya ce duk da cewa mutanen Biritaniya sun gwammace a kona gawarsu, hakan bai hana matsalar yin kamari ba.

"Kananan hukumomi biyu a birnin London - Tower Hamlets da Hackney – sun daina bayar da izinen binne matattu. Mazauna wajen na zuwa wasu unguwanni da ke makwabtaka da su ne don binne mutane."

Mr Morris ya ce da fari mutanen Biritaniya suna jin al’amarin wani banbarakwai, amma a yanzu ya zama jiki.

'Sake amfani da tsofaffin makabartu'

Wani bincike da aka yi a shekarar 2013, ya gano cewa nan da shekaru 20 za a rasa wajen binne mutane a rabin makabartun Ingila .

Mafita guda daya ita ce a dinga binne mutane a makabartun da tuni suka cika, ta hanyar dago tsofaffin gawawwaki a mai da su can kasa, tare da binne sabbin gawawwakin daga sama-sama.

Karuwar karancin wajen binne gawa dai matsala ce da ke damun hukumomi a duniya.

Sauran kasashen nahiyar Turai kamar su Jamus, tuni suka fara amfani da tsoffin makabartu wajen binne gawawwaki.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yaro mai bin addinin Hindu zai zubar da tokar mahaifinsa

Iyalai a Sifaniya da Girka kuwa suna hayar wani wuri da ake ajiye gawar mutum kamar a kan tebur na tsawon shekaru da har za ta rube.

Idan gawar ta rube sai a dauke ta zuwa wajen binne gawa, ta yadda za a sake bayar da hayar wancan wajen.

Haka ita ma makabartar tsibirin Venice San Michelle a na bayar da hayarta, inda ake dauke gawawwaki bayan sun rube.

Isra’ila kuwa ta amince da gina dogon gini mai dauke da ginin karkashin kasa, koda yake yahudawa ‘yan usuli suna adawa da hakan.

A mafi yawan bangarorin duniya da suke da mutane da yawa, an fi kona gawa, amma mutane da dama na samun matsala ta samun filin da za su adana tokar ‘yan uwansu.

A Hong Kong, dubban iyalai ba su da mafitar da ta wuce adana tokar ‘yan uwansu a cikin buhunhuna su ajiye a gida, yayin da za su jira tsawon lokaci don samun wajen binne tokar.

A Singapore, wani kamfani mai zaman kansa yana ajiye akwatinan gawa domin a biya shi.

Indiya wacce ita ce kasa ta biyu da mafi yawan al’umma a duniya, mabiya addinin Hindu a kasar na barbada tokar gawa ne bayan sun kona, amma musulmai da kiristocin kasar na fuskantar matsalar karancin wajen binne gawarwakin ‘yan uwansu.

Sauran kuwa na duba yiwuwar amfani da bangarorin kimiyya da dama ne domin samun mafita, a cewar Tim Morris.

An amfani da wata hanya da ake kira 'Resomation' ta yin amfani da sinadiri wanda zai narkar da gawar watau ta rabarbashe ta zama toka da ruwa.

"A yanzu dai an haramta wannan tsarin a Ingila, amma Scotland na duba yiwuwar hakan."

Abin da hakan ne nuna wa shi ne dai baya ga tunanin mutuwa matsalar inda za a binne gawa ma ta shiga sawun abin taraddadi.