Rikici: An rufe makarantu a Chadi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An rufe makarantun ne saboda dalibai sun yi bore

Hukumomi a kasar Chadi sun rufe dukkan makarantu, cikinsu har da jamio'i bayan wani mummunan bore da ya kai ga mutuwar akalla mutane uku.

Dalibai sun yi bore ne domin bijirewa wata sabuwar dokar hular kwano da hukumomi suka ce dole kowanne mai babur ya rika sanya wa

Da dama daga cikin 'yan kasar dai suna adawa da dokar, suna masu cewa sanya hular kwanon yana sa wa su ji zafi, sannan tana da tsada a kasuwa.

Farashin hular kwanon dai ya yi tashin gwauron-zabi tun lokacin da aka sanya dokar a farkon wannan watan.

'Yan kasar ta Chadi na yin amfani da babura da motocin tasi sosai domin yin kai-komo.