Dakaru sun yi wa birnin Tikrit zobe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gwamnatin Iraki na samun goyon bayan mayakan sa-kai 'yan Shi'a

Dakarun gwamnatin Iraki tare da goyon bayan mayakan 'yan Shi'a sun yi wa birnin Tikrit zobe a kokarinsu na kwace garin daga mayakan kungiyar IS.

Hukumomin Iraki sun ce dakarunsu da mayakan sa-kai 'yan Shi'a sun kwace garin Alam da ke kusa da Tikrit.

Rahotanni sun ce mayakan IS sun fasa wata gada da ra ratsa ta kogin Tigris abin da zai bai katse hanzarin dakarun gwamnati.

Kokarin kwace garin Tikrit shi ne gumurzu mafi girma da gwamnati ke yi da masu da'awar Jihadi.

Fafatawar da ake a yanzu na samun goyon bayan dakarun kasar Iran amma babu taimakon Amurka.