Ana tallan jarirai a China

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata ta bukaci wakilin BBC ya sayi jaririnta

Wani bincike da BBC ta gudanar ya nuna cewa ana yin tallan jarirai ta shafukan intanet na China duk da yunkurin 'yan sandan kasar na kawar da safarar kananana yara.

A wasu lokutan masu yin wannan sana'a suna fakewa da cewa suna karbar yaran ne domin rainonsu.

Wani talla da aka yi a shafin na intanet ya bukaci a sayi wani jariri dan watanni takwas a kan $30, 000.

Ma'aikacin BBCn da ya yi binciken ya bayyana kansa ne a matsayin wanda ke son sayen jarirai, kuma wata mata -- wacce ta ce mijinta ya rasu domin haka ba za ta iya rainon dansu ba -- ta yi masa tallan dan nata.

Koda yake an halasta yin tallan yara ga masu son yin rainon a kasar ta China, amma sayar da su domin manufa ta daban ya saba wa dokar kasar.

Bincike ya nuna cewa kimanin kananan yara 20, 000 ake sacewa a kasar a duk shekara, kuma mutane da dama sun yi amanna ana sayar da yaran ne.