Ana zargin tsohon Firayi Ministan India da cin hanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Manmohan Singh ya ce bai ji dadin sammacin da kotu ta yi masa ba

Wata kotu a India ta bukaci tsohon Firayi Ministan kasar, Manmohan Singh, ya gurfana a gabanta bisa zargin cin hanci a batun bayar da izinin hakar kwal ba bisa ka'ida ba.

Wannan batu dai shi ne zargin cin hanci mafi girma da aka yi a kasar ta India.

Ana zargin cewa an gwamnatin kasar -- a wancan lokacin -- ta sayar da wuraren hakar kwal masu yawa ba bisa ka'ida ba, lamarin da ya janyo wa kasar asarar biliyoyin dala.

A lokacin dai Manmohan Singh ne ministan ma'aikatar hakar kwal.

Sai dai a baya kamfanin CBI, wanda ya gudanar da bincike kan batun, bai same shi da laifi ba.

Mr Singh ya ce bai ji dadin sammacin da kotun ta aike masa ba, yana mai musanta hannu a batun na cin hanci.