Iran ta na son mata su rinka haihuwa

Image caption Yawanci al'ummar Iran tsofaffi ne

Kungiyar kare hakkin dan-adam ta Amnesty International ta soki yunkurin da Iran take na karfafawa mata gwiwa domin su kara haihuwar 'ya'ya.

Wata doka da aka gabatar zata haramta bayyanawa jama'a hanyoyin takaita iyali.

Zai kuma yi wahala ga duk matar da bata da 'ya'ya ta samu aikin yi a daya daga cikin dokokin , har ila yau sakin- aure zai kasance abu mai matukar wahala

Amnesty ta bayyana dokokin a matsayin komabaya ga 'yancin na mata.

Wakiliyar BBC tace a baya dai Iran na goyan bayan takaita iyali, amma a yanzu hukumomi sun damu kasancewar tsofaffi sun fi yawa a al'ummar kasar.