Saudiya ta janye jakadanta daga Sweden

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Saudiya ta hana ministar harkokin wajen Sweden yin magana a taron kasashen Larabawa.

Saudi Arabia ta janye jakadanta daga kasar Sweden sakamakon tsamin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sweden Erik Boman, ya ce Saudiyan ta fusata ne saboda sukar da Sweden din ke mata a kan take hakkin bil adama.

Kakakin ya ce Sweden ba ta da wani shiri na janye jakadanta daga Saudiyan, yana mai cewa "huldar diplomasiyya ba ta lalace ba tsakaninmu."

Dangantakar ta fara tsami ne a wannan makon, yayin da Sweden ta soke wata dadaddiyar yarjejeniya ta hadin gwiwa kan harkar soji tsakanin kasashen biyu, bayan ta zargi Saudiyan da hana ministar harkokin wajen Sweden din yin magana a kan dimokradiyya da kuma 'yancin mata a wani taron kasashen Larabawa.

Yarjejeniyar da Sweden take sayar wa Saudiya makamai na miliyoyin daloli za ta zo karshe ne a watan Mayu.