Bangladesh: Gini ya rufto, ya kashe mutane 5

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ana cigaba da aikin ceto mutane da ginin ya danne.

'Yan sanda a Bangladesh sun ce mutane biyar ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman wasu da yawa bayan da bangaren wani gidan da ake ajiyar simunti ya rufto musu.

Kimanin magina 100 ne ke cikin ginin wanda ba a karasa shi ba la okacin da lamarin ya afku.

Zuwa yanzu dai an ciro fiye da mutane 40, wasu daga cikinsu sun samu raunuka.

Gidan ajiyar sumintin dai mallakin wata hukumar jin dadin sojin kasar ce a garin tashar jiragen ruwa ta Mongla da ke kudu maso yammacin babban birnin kasar, Dhaka.