Mun kusa kwato 'yan matan Chibok — Sambo

Alhaji Namadi Sambo.
Image caption Fiye da shekara guda kenan da kungiyar Boko Haram ta sace 'yan matan sakandaren Chibok.

Gwamnatin Nigeria ta ce ba za a kara daukar wani dogon lokaci ba wajen kubutar da 'yan matan Chibok da 'yan kungiyar Boko Haram suka sace.

Mataimakin shugaban kasar ne ya bayyana haka a yayin tattaunawar su da BBC a lokacin da ya kai ziyara a Kano.

Namadi Sambo ya kuma yi da'awar cewa babu wata gwamnati da ta yi yaki da cin hanci da rashawa da ta kai gwamnatinsu, inda ya bayyana cewar a kokarin da gwamnatin PDP ke yi na kawar da matsalar cinhanci da rashawa an samu mutane sama da 100 da laifi, ya yin da aka yankewa sama da 400 hukunci.

Har wa yau, ya ce sun yi nasarar karbo makudan kudaden da aka yi sama da fadinsu, duk dai a kokarin magance wanann matsala.

Dangane da zabe kuma, ya ce jam'iyyarsu ba ta tsoron a yi amfani da na'urar tantance masu kada kuri'a sai dai suna so a yi adalci.