An harbi 'yan sanda biyu a Ferguson

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An harbi 'yan sandan ne a fuska da kafada

An harbi 'yan sanda biyu a birnin Ferguson na Amurka, inda aka yi ta samun tashe-tashen hankula tun bayan kashe wani bakar fata da wani dan sanda farar fata ya yi a watan Agustan bara.

An harbi daya daga cikin ‘yan sandan ne a fuska yayin da dayan kuma aka harbe shi a kafada.

Rundunar 'yan sandan birnin ta ce jami'an nata da aka harba suna asibiti inda ake duba su.

Wani ganau ya shaida wa BBC cewa ya ga 'yan sandan a kwance face-face cikin jini.

An dai harbi 'yansandan ne a wajen ofishinsu, inda masu zanga-zanga suka taru bayan shugaban rundunar 'yan sandan, Thomas Jackson, ya sanar da cewa ya yi murabus.

Wani rahoto da aka fitar ya zargi rundunar 'yan sandan da nuna wariyar launin fata.

A farkon makon nan ne wani alkali a Ferguson ya yi murabus.