Dakarun Iraki sun kara dannawa cikin Tikrit

Sojin Iraki

Wasu majiyoyin tsaro a kasar Iraki sun ce dakarun gwamnati sun kara samun galaba a kokarin da suke yi na sake kwato birnin Tikrit daga mayakan IS.

Rundunar Sojin kasar ta ce da tsakar daren jiya ne dakarunta suka mamaye arewaci, da gabashi da kuma yammacin tsakiyar birnin.

Kamar yadda rahotanni suka nuna akwai kimanin mayakan IS dari da hamsin da suka rage a Tikiri din.

Muddin kuma dakarun gwamnati za su iya fatattakar daukacin mayakan wata gagarumar nasara ce a birnin mai matukar muhimmanci.

Birnin na Tikrit shi ne mahaifar tsohon shugaban kasar ta Iraki, Saddam Husain.