IS ta amince da Boko Haram

Jagoran kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi Hakkin mallakar hoto AP
Image caption A makon da ya wuce ne jagoran kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, ya sanar da mubaya'ar ga kungiyar ga IS.

Kungiyar da ke fafutukar kafa daular Musulunci IS ta amince da mubayi'ar da kungiyar Boko Haram ta Nigeria ta yi mata

A wani sakon murya da aka nada, sanna aka wallafa ta reshen hulda da 'yan jarida na kurgiyar IS mai suna Al-furgan, mutumin da ya yi ikirarin yana magana da yawun shugaban kungiyar Abu Bakr al-Baghdadi, ya yi ikirarin cewa wannan mubaya'a da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya yi alama ce da ke nuna jihadin da IS ke yi ya fadada zuwa yammacin Afirka.

Wannan na zuwa ne kasa da mako guda da kungiyar Boko Haram ta wallafa sakon muryar a shafin ta na Twitter, inda jagoranta ke cewa sun yi mubaya'a da IS.

Al-adnani ya bukaci mayakan sa-kai su yi hijira tare da shiga kungiyar Boko Haram domin taimaka mata wajen ayyukan da take yi.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane dubu 10 a shekarar 2014, sannan ta yi sace 'yan mata 200 na makarantar Chibok.