IS na amfani da iska mai guba wajen hada bom

Hakkin mallakar hoto AP

BBC ta ga wata hujja da ke nuna cewa mayakan IS na amfani da iskar gas mai guba ta 'Chlorine' a matsayin wani makami a filin daga a Iraqi.

Gwamnatin Iraqi ta ce IS na amfani da wannan iska mai guba 'yar kadan wajen hada bama- baman da ake dasawa a bakin titi, da nufin kashe dakarun kasar da ke kokarin fatattakkar mayakan IS daga Tikrit.

A wani bidiyon da masu kwance irin wadannan bama- bamai na Iraqi suka nunawa BBC, ya nuna yadda irin wadannan bama bamai ke fitar da wani hayaki mai kauri launin lemo zuwa sararin samaniya.

Kwararru a kan makamai masu guba sun yi imanin cewa an tsara amfani da irin wadannan bama- baman ne domin su yi lahani a jikin bil adama.