Kaduna: APC na zargin PDP da bata dan takararta

Image caption Malam Nasiru El-Rufa'i, dan takarar gwamnan Kaduna a jam'iyyar APC

Jamiyyar APC a jihar Kaduna ta nuna damuwa a bisa abin da ta kira kokarin bata wa dan takarar ta na gwamna suna ta fuskar addini.

'Ya'yan APCn na zargin 'yan jam'iyyar PDP musamman masu neman sake zaben gwamnan jihar da bugawa tare da raba kasidu ga kiristoci don ganin sun juyawa dan takarar su Malam Nasiru El Rufai baya.

Mr Samuel Aruwan shi ne kakakin Malam Nasiru El-Rufa'i ya kuma ce: ”Akwai takardu da ake rabawa na batanci a inda mutane ke ibada don a nuna musu cewa dan takararmu ba ya kaunar wadanda ba Musulmi ba, kuma mun san 'yan PDP ne suke aikata hakan.”

Sai dai a nasa bangaren, Mallam Yakubu Lere kakakin kwamitin yakin sake neman zaben gwamna Mukhtar Yero, musanta zargin yayi, yana mai cewa: "wannan abu ya bani mamaki yau ne kuma ake cewa PDP na amfani da addini, bayan mu da muke 'yan PDP kafurta mu ma ake yi amma muke hakuri. Wannan shure-shure ne da baya hana mutuwa da ‘yan APC ke yi."

Ana zargin 'yan siyasa a Nigeriar a sassa daban-daban na kasar na cigaba da amfani da addini don neman samun goyon baya, abinda wasu ke cewa bai dace domin hakan yana kawo rarrabuwar kan al'umma.