Bauchi: Sojin Najeriya sun fatattaki Boko Haram

Hakkin mallakar hoto
Image caption Rundunar sojin Nigeria na cigaba da kokarin kawo karshen hare-haren kungiyar Boko Haram

Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun tarwatsa wasu sansanonin mayakan Boko Haram a cikin wani daji a jihar Bauchi dake arewa maso gabashin kasar.

Hukumomin sun ce sojoji sun kaddmar da samame ne kan mayakan Boko Haram din a dajin Lame zuwa Burra, daga karshen makon jiya zuwa tsakiyar wannan mako, kuma sun bayyana cewa masu tayar da kayar baya da dama sun rasa rayukansu a lamarin.

Dakarun sojin runduna ta 33 ne suka kai samamen a dajin, wanda yake tsakanin karamar hukumar Toro da karamar hukumar Ningi ta jihar.

A wata sanarwa da ta fito daga rundunar sojin mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin jami'in hulda da jama'a na rundunar Kanal Sani Kuka-Sheka, ba ta fadi adadin 'yan Boko Haram din da aka kashe ba, bata kuma sanar da ko akwai jami'an tsaron da suka rasa rayukansu ko su jikkata ba.