Tanzania: An kama matsafa 200 a kan kisan zabiya

Image caption Gwamnatin Tanzania na cigaba da kokarin hana kisan zabiya a kasar.

An kama matsafa fiye da 200 a kasar Tanzania a wani yunkuri na hana kisan da ake yi wa zabiya.

Matsafan na amfani da bangarorin jikin zabiyan ne wajen yin tsafi da nufin hakan zai kawo arziki da cigaba.

'Yan sanda sun ce wasu daga cikin matsafan da aka kama, an same su da fatar namun daji da kuma wasu kayan tsafi.

Gwamnatin kasar dai ta samar wa zabiya da wata na'ura da suke rike wa a hannayensu, wacce kan yi ihu a duk lokacin da aka kai musu hari.

Majalisar Dinkin duniya ta ce zabiya akalla 76 ne aka kashe a Tanzania tun a shekarar 2000.

A kasar Malawi ma da ke makwabtaka da Tanzaniyar, 'yan sanda sun ce sun kama wani mutum da yake yunkurin kashe wani zabiya.