Twitter ta sake sabbin tsare-tsare

Twitter Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Twitter ya dauki wannan mataki ne, dan hana masu sanya hotunan tsiraici a shafin.

Shafin sada zumunta da muhawara na Twitter ya fito da sabbin tsare-tsare, a kokarin hana masu wallafa hutunan tsiraici na daukar fansa.

A karkashin sabuwar dokar ba a mince a wallafa hotuna ko bidiyon da aka dauka ba don a sanya a shafukan sada zumunta ba.

Hotunan da aka wallafa a shafin a watan da ya gabata dai sun zama babban laifi a Burtaniya da Wales.

Mai magana da yawun kamfanin Twitter ya ce, duk wadanda suka ketare wannan sabuwar doka, to la budda za a rufe musu shafin su dungurugum.

Ya yin da su kuma wadanda sukai korafin an wallafa hotunan su da bidiyo, za a bukaci su bada bayanan da suka shafe su, da kuma tabbacin ba su bada damar a yada su ba.

A bangare guda kuma duk wanda ya wallafa irin wadannan hotuna da bidiyo, za a buka ci ya goge su kafin ya samu komawa ainahin shafin da yake.

Wata kotun hukunta muggan laifuka a Burtaniya da Wales, ta zartar da hukunci daurin shekaru biyu ko ma fiye da haka ga duk wanda aka samu da laifin wallafa hotunan tsiraici a shafin Twitter.

Haka kuma dokar ta shafi hotunan da aka tura ta shafukan sada zumunta da muhawa, da kuma sakon text.